Watch and track your favorite playlist.
Curated by: HausaFilmsTV (302 videos)
Ƙarin bayani: https://hausadictionary.com/HausaRadio.net/2026-06-05 == BBCHausa Safe 2026-06-05 == Mai gabatarwa: Imam Saleh 🎧@0:22 Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya yi magana kai tsaye da ƙungiyar Hezbollah kan yiwuwar kawo ƙarshen rikicin da ake yi a Lebanon. 🎧@0:30 Wani kamfanin fasahar AI ya yi gargaɗin cewa sabbin fasahohin da yake samarwa sun fara nuna alamun ƙangarewa umarnin ɗan Adam. 🎧@0:40 A Najeriya, jam’iyyar APC mai mulki ta yi ƙarin haske kan tsikon bayar da shaidar cin zaɓen cikin gida ga wasu ’ya’yanta, lamarin da ya sa wasu ke fargabar za a iya ƙwace musu takara. 🎧@1:07 A birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, an ƙaddamar da wata tashar samar da wutar lantarki ta haɗin gwiwa tsakanin ƙasar da Aljeriya. 🎧@1:28 Manoman Najeriya sun fara nuna damuwa kan tsadar taki da kuma faɗuwar farashin amfanin gona. == BBCHausa Hantsi 2026-06-05 == Mai gabatarwa: Imam Saleh 🎧@1:58 Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya wallafa wata buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga takwaransa na Rasha Vladimir Putin. 🎧@2:15 Wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ya nuna cewa yara ’yan ƙasa da shekara biyar na fuskantar kusan ninki uku na haɗarin kamuwa da cututtukan da ake samu daga abinci marar tsafta idan aka kwatanta da manya. == BBCHausa Rana 2026-06-05 == Mai gabatarwa: Aisha Aliyu Jafar 🎧@3:29 Ukraine ta ce ta kai hare-hare kan wasu jiragen ruwa da ake ɗaukon hatsin da Rasha ta sata daga sassan da ta mamaye a ƙasar. 🎧@3:37 Gwamnatin sojan Mali ta haramta amfani da babura a wajen manyan biranen ƙasar domin dakile ayyukan masu ɗauke da makamai. 🎧@3:44 A jihar Bauchi ta Najeriya, ƙura ta lafa bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a wasu garuruwa. 🎧@4:06 Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta ce shirye-shirye sun yi nisa wajen samar da ’yan sandan jihohi domin shawo kan matsalar tsaro. == DWHausa Safe 2026-06-05 == Mai gabatarwa: Binta Aliyu Zurmi 🎧@5:11 A Najeriya, baraka ta ɓarke a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa. 🎧@5:23 A ranar kare muhalli ta duniya, DW za ta je Najeriya domin jin yadda batun kare muhalli yake a ƙasar. 🎧@5:29 Hukumomi a jihar Tawa ta Jamhuriyar Nijar sun haramta sayar da man fetur a kasuwannin bayan fage. 🎧@5:36 A ƙasar Mali, za a ji yadda matsalar man fetur ke ci gaba da yin ƙamari. 🎧@6:00 Hukumar IAEA ta buƙaci kai ziyara tashoshin nukiliyar Iran. == DWHausa Rana 2026-06-05 == Mai gabatarwa: Fauziyya Dauda 🎧@6:44 Jamus da Ƙungiyar Tarayyar Turai EU sun ƙaddamar da wani shiri na kula da albarkatun ruwa a yankin Tafkin Chadi da nufin kare muhalli da inganta rayuwar al’umma. 🎧@7:00 A Najeriya, Majalisar Wakilai ta fara bincike kan zargin yadda jam’iyyu suka karya dokokin zaɓe yayin zaɓukan fitar da gwani. 🎧@7:10 Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar, Abdourahamane Tchiani, na kammala ziyarar aiki a ƙasar Turkiyya bayan ƙasashen biyu sun sanya hannu kan yarjejeniya a fannoni daban-daban. 🎧@7:48 Kishirwa da tsananin zafi sun halaka matafiya kusan hamsin bayan lalacewar motarsu a saharar Nijar. == DWHausa Yamma 2026-06-05 == Mai gabatarwa: Fauziyya Dauda 🎧@8:41 Armenia za ta gudanar da zaɓen ’yan majalisar dokoki a wannan watan, zaɓen da zai saita akalar siyasar ƙasar da ke goyon bayan Rasha. 🎧@9:11 Kotun Amurka ta soke dokar da Shugaba Trump ya kafa da ta haramta wa ’yan ƙasashe talatin da tara ’yancin zama Amurkawa. 🎧@9:24 Kotun Mali ta ɗaure wani Bafaranshe da ta zarga da leƙen asiri. == CRI / CGTN Hausa 2026-06-05 == Mai gabatarwa: Nifaiza Muhammad Mustafa 🎧@9:49 Shugaban ƙasar Sin, Xi Jinping, zai kai ziyarar aiki Koriya ta Arewa. 🎧@9:54 Ma’aikatar kasuwanci ta Sin za ta gudanar da bukukuwa fiye da ɗari na shiri mai taken “Fitar da kayayyaki zuwa ƙasar Sin” a bana. 🎧@10:05 Gwamnatin Najeriya ta buƙaci kafofin yaɗa labarai, hukumomin tsaro, da ƙungiyoyin al’umma su haɗa kai wajen yaƙar aikata ta’addanci a ƙasar.