Uploads from HausaFilmsTV

Watch and track your favorite playlist.

Curated by: HausaFilmsTV (302 videos)


Currently Playing: Kanun Labaran Hausa na 2026-07-08 (HausaRadio.net News Headlines)

Ƙarin bayani: https://hausadictionary.com/HausaRadio.net/2026-07-08 == BBCHausa Safe 2026-07-08 == Cikakken shiri: https://www.bbc.com/hausa/bbc_hausa_radio/w3ct954x Mai gabatarwa: Raliha Zubairu 🎧@0:15 To a cikin shirin za ku ji cewa an sake samun barkewar faɗa tsakanin Amurka da Iran. 🎧@0:20 Wasu ƙasashen Turai goma sha biyu za su samar da wani sabon makami mai linzami mai cin dogon zango domin kare yankin Turai. 🎧@0:30 A Najeriya, majalisun dokokin tarayya sun kira ga gwamnatin ƙasar ta dakatar da shirin sauya tunanin tubabbun 'yan Boko Haram da 'yan bindiga. == BBCHausa Hantsi 2026-07-08 == Cikakken shiri: https://www.bbc.com/hausa/bbc_hausa_radio/w1730mcn2jrbxdl Mai gabatarwa: Raliha Zubairu 🎧@1:50 Ƙungiyar agaji ta Save the Children ta ce yara fiye da dubu biyar ne suka rasa mahallansu a birnin El-Obeid na ƙasar Sudan a cikin makonni biyu da suka gabata. 🎧@1:59 A Najeriya, hukumar kula da harkokin shari'a a jihar Kano ta yi ƙarin haske game da matakin da ta ɗauka na ɗaukar matakin ladabtar da wasu ma'aikatanta ciki har da alƙalai. == BBCHausa Rana 2026-07-08 == Cikakken shiri: https://www.bbc.com/hausa/bbc_hausa_radio/w3ct94x0 Mai gabatarwa: Haruna Shehu Tangaza 🎧@3:36 BBC Rana ta ce Shugaba Donald Trump ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar Amurka da Iran ta ƙare yanzu, yana mai bayyana ta a matsayin ɓataccen abu tare da yin gargaɗin cewa Amurka za ta kai wa Iran munanan hare-hare cikin daren yau. 🎧@3:55 Ƙoƙarin da ake na samun haɗin kai da kuma baki ya zo ɗaya a taron ƙolin ƙungiyar NATO kuwa ya samu cikas sakamakon ci gaba da sukar ƙasashen Turai da Shugaba Trump ɗin ke yi. 🎧@4:37 A Najeriya kuwa aƙalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a cikin wani sabon harin 'yan bindiga a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar, kuma wani ganau ya ce sun sace ɗimbin dabbobi. == BBCHausa Yamma 2026-07-08 == Cikakken shiri: https://www.bbc.com/hausa/bbc_hausa_radio/liveradio Mai gabatarwa: Haruna Shehu Tangaza 🎧@6:18 A Najeriya, ƙungiyar gwamnonin jihohin arewacin ƙasar ta ƙaddamar da wani kwamitin amintattu da za su jagoranci tafiyar da gidauniyar ayyukan samar da tsaro ta yankin Arewa da gwamnonin suka kafa. == DWHausa Safe 2026-07-08 == Cikakken shiri: https://www.dw.com/ha/shirin-safe-08072026/audio-77871423 / https://www.youtube.com/watch?v=3E3U4Gc_V2M Mai gabatarwa: Musa Tijjani Ahmad 🎧@8:56 DW Labaran Duniya ta ce Amurka ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a Iran a daidai lokacin da ake ci gaba da jana'izar Ayatollah Ali Khamenei; mambobin ƙasashen NATO za su fara taronsu a birnin Ankara na Turkiyya; 'yan sandan Afirka ta Kudu sun kama masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba sama da ɗari biyu da galibinsu 'yan ƙasashen ƙetare ne. == DWHausa Rana 2026-07-08 == Cikakken shiri: https://www.dw.com/ha/shirin-rana-08072026/audio-77880372 / https://www.youtube.com/watch?v=MON07OsEMLA Mai gabatarwa: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim == DWHausa Yamma 2026-07-08 == Cikakken shiri: https://www.dw.com/ha/shirin-yamma-08072026/audio-77882264 / https://www.youtube.com/watch?v=f7ciGV_qbdU Mai gabatarwa: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim == RFIHausa 0600GMT 2026-07-08 == Cikakken shiri: https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/06h00-06h17-gmt/20260708-labarai-08-07-06h00-gmt?GJlXzGgqHj Mai gabatarwa: Ahmad Abba 🎧@13:41 RFI Hausa 0600GMT ta ce Amurka da Iran sun sake kai wa juna munanan hare-hare, lamarin da ke ƙara fargabar dawowar yaƙi da kuma farashin mai a kasuwannin duniya; Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gudanar da bincike kan hukumar bogi da ake zargi an ƙirƙire ta ba tare da sa hannun fadar shugaban ƙasar ba; Shugaban ƙasar Senegal ya garzaya kotun kundin tsarin mulki domin ƙalubalantar gyaran kundin tsarin mulki da aka yi wanda ke rage ƙarfin ikon shugaban ƙasa. == RFIHausa 0700GMT 2026-07-08 == Cikakken shiri: https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/07h00-07h17-gmt/20260708-labarai-08-07-07h00-gmt?GJlXzGgqHj Mai gabatarwa: Ahmad Abba 🎧@14:40 RFI Hausa 0700GMT ta ce Amurka da Iran sun sake kai wa juna munanan hare-hare lamarin da ke ƙara fargabar dawowar yaƙin; hukumar zaɓe INEC a Najeriya ta samar da hanyoyin rajista daga gida waɗanda za su yi rajistar katin zaɓe; rukunin kamfanonin hamsakin attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana shirin gina matatar mai a ƙasar Kenya wadda za ta riƙa tace ganga dubu ɗari bakwai a kowace rana. == RFIHausa 1600GMT 2026-07-08 == Cikakken shiri: https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/labarai-16h00-16h30-gmt-litinin-jumma-a/20260708-labarai-08-07-16h00-gmt?GJlXzGgqHj Mai gabatarwa: Michael Kudison == CRI / CGTN Hausa 2026-07-08 == Cikakken shiri: https://hausa.cri.cn/2026/07/08/AUDI1783495435460676


Tracks in this Playlist