Uploads from HausaFilmsTV

Watch and track your favorite playlist.

Curated by: HausaFilmsTV (302 videos)


Currently Playing: Kanun Labaran Hausa 2026-06-01 (HausaRadio.net News Headlines)

Visit https://hausaradio.net for the story links in full, and to get our daily newsletter. Ƙarin bayani: https://hausadictionary.com/HausaRadio.net/2026-06-01 == BBCHausa Safe 2026-06-01 == Mai gabatarwa: Imam Saleh 🎧@0:26 Wani ɗan siyasa mai ra’ayin mazan jiya da ba a sani sosai ba ya yi nasara a zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasar Colombia. 🎧@0:35 Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce gwamnatinsa na da hujjojin da ke nuna cewa Rasha na horas da yaran Ukraine da aka sace domin su yaƙi ƙasarsu ta asali. 🎧@0:45 A Najeriya, tsohon gwamnan jihar Bauchi, kuma ɗan takarar gwamnan jihar a zaɓen 2023 na APC, M.A. Abubakar, ya ce zafin kai ne ya sa wasu da suka nemi takara tare da shi ke zargin an yi rashin adalci. 🎧@1:15 Masana a fannin ilimi a Najeriya na ci gaba da nuna damuwa kan yadda iyaye ke zaɓawa yara fannonin da za su karanta a jami’o’i ba tare da la’akari da abin da suke da sha’awa ba. == BBCHausa Hantsi 2026-06-01 == Mai gabatarwa: Imam Saleh 🎧@2:12 Hotunan tauraron ɗan adam na bidiyo da BBC ta tantance sun nuna cewa Iran ta lalata wuraren sojin Amurka guda ashirin a ƙasashe takwas na Gabas ta Tsakiya. 🎧@2:26 Hukumomin lafiya a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo sun yi murnar warkewar mutum biyar da suka tsira daga cutar Ebola. 🎧@2:42 A Najeriya, masana tsaro sun bayyana damuwa kan girman matsalar tsaron da ke damun ƙasar bayan da wasu ’yan bindiga da ba a tantance su ba suka sace wani tsohon janar na soja. == BBCHausa Rana 2026-06-01 == Mai gabatarwa: Rabi’at Rinƙace 🎧@4:03 Isra’ila ta ba da umarnin kai hare-hare kan Hezbollah a yankunan kudancin Lebanon. 🎧@4:16 A Najeriya, ɗaruruwan malaman makaranta, iyaye, da ƙungiyoyin matasa sun fantsama titunan jihar Oyo domin yin zanga-zanga. 🎧@4:39 A Jamhuriyar Nijar, hukumomi a birnin Yamai sun ƙaddamar da wani gagarumin aikin rusau, yayin da al’ummar da abin ya shafa suka bayyana yadda suka ji. == BBCHausa Yamma 2026-06-01 == Mai gabatarwa: Rabi’at Rinƙace 🎧@5:56 Alamu na nuna cewa Amurka da Iran na son kawo ƙarshen yaƙin da suke yi bayan dukkan ɓangarorin suka ci gaba da ba da haɗin kai a tattaunawar zaman lafiya. 🎧@6:30 Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa ’yan bindiga sun buɗe wa masallata wuta a daren jiya. == DWHausa Safe 2026-06-01 == Mai gabatarwa: Musa Tijjani Ahmad 🎧@7:20 Dangantaka tsakanin Amurka da Taiwan ta kasance ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka sa aka shafe shekaru masu yawa ana zaman tankiya tsakanin Amurka da China. 🎧@7:36 Gwamnatin Najeriya ta jaddada aniyarta ta yaƙi da ’yan fashin teku a Legas. 🎧@8:37 An buɗe rumfunan zaɓen shugaban ƙasa a ƙasar Habasha. == DWHausa Rana 2026-06-01 == Mai gabatarwa: Khadija Ahmad Rufa’i 🎧@9:19 A Tarayyar Najeriya, muhawara ta ɓarke kan sabon mafi ƙarancin albashi. == DWHausa Yamma 2026-06-01 == Mai gabatarwa: Khadija Ahmad Rufa’i 🎧@11:29 Firayim Ministan Hungary ya ce zai ɗauki matakin sauke shugaban ƙasar daga muƙaminsa idan har bai yi murabus ba. 🎧@11:44 Kotu ta yi watsi da buƙatar Rwanda ta neman diyya kan dakatar da tura masu neman mafaka zuwa ƙasar a ƙarƙashin tsarin tsohuwar gwamnatin Birtaniya. == RFIHausa Safe 2026-06-01 == Mai gabatarwa: Umma Rusani 🎧@12:35 Amurka ta bai wa Nijar tallafin kayan soji da darajarsu ta kai sama da dala biliyan guda, irinsa na farko cikin shekaru biyu. == CRI / CGTN Hausa 2026-06-01 == Mai gabatarwa: TBD 🎧@14:17 Asusun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ƙasar Sin ta cimma manyan nasarori a fannin bayar da hidima ga yara masu buƙata ta musamman.


Tracks in this Playlist